Manoman tumatur a Kano sun yi asarar kusan biliyan 2 saboda wata tsutsa
Manoman tumatir a jihar Kano da ke Najeriya sun tafka asarar sama da Naira biliyan 1 da biliyan 500 kuma har yanzu suna ci gaba da kidayar asarar wadda wata shu'umar tsutsa ta haddasa musu.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:09
Talla
Tsutsar da ake kira 'Tuta Absaluta' ta lalata gonakan tumatiri da dama, lamarin da ya durkusar da manoman sama da dubu biyar a jihar.
Wannan ibtila'in ya haifar da karancin tumatur a sassan jihar Kano da kewaye.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Abubakar Isa Dandago daga Kano.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu