Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta kwashe daukacin 'yan kasar daga Sudan

Gwamnatin Najeriya ta ce, ta yi nasarar kwashe daukacin 'yan kasar da suka makale a babban birnin Khartoum na kasar Sudan mai fama da tashin hankali.

Tawaga ta biyu ta 'yan Najeriya daga Sudan ta isa Abuja da misalin karfe 3 da minti 10 na ranar Juma'a
Tawaga ta biyu ta 'yan Najeriya daga Sudan ta isa Abuja da misalin karfe 3 da minti 10 na ranar Juma'a REUTERS - Afolabi Sotunde
Talla

Sakataren din-din a Ma'aikatar Jin-kai ta Najeriya, Dr. Sani Gwarzo ya bayyana haka a yayin tarbar tawaga ta biyu mai kunshe da mutane 130 da ta isa filin jiragen sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikwe da ke birnin Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya rawaito cewa, mutanen sun iso ne da misalin karfe 3 da minti 10 na rana agogon Najeriya a ranar Juma'a daga Port Sudan.

Tawagar ta kunshi maza biyu kacal, sai kuma sauran adadin da ya hada da mata da kananan yara.

Ina farin cikin sanar da cewa, mun yi nasarar kwashe kowa da kowa da ke bukatar a dauke shi daga Khartoum, babu mutun daya daga cikin 'yan uwanku a yau da ke cikin Khartoum, an kwashe su baki daya. Inji Dr. Gwarzo

Kodayake har yanzu akwai dimbin 'yan Najeriya da ke ci gaba da kasancewa a kan iyakar kasar Masar.

Amma Dr. Gwarzo ya bayyana kwarin guiwar kwaso su zuwa gida nan da kwanaki kalilan masu zuwa.

An dai bai wa mutanen tallafin Naira dubu dari-dari da watakila za su yi amfani da shi wajen sake koma cikin iyalansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.