Isa ga babban shafi

Najeriya: 'Yan bindiga sun yi kwanaki suna addabar al'ummar Shinkafi a Zamfara

A Najeriya ‘yan bindiga sun bindige mata biyu har lahira a yayin da suka tare hanyar Katuru mai nisan kilomita 2 zuwa kwaryar garin karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara a yau Lahadi.

Zamfara na cikin tashin hankalin hare-haren 'yan bindiga
Zamfara na cikin tashin hankalin hare-haren 'yan bindiga © Channels
Talla

Majiyoyi daga yankin sun shaida wa RFI hausa cewa har ya zuwa lokacin da ake wannan zance, gawarwakin  matan da aka kashe na kwance a hanyar ba a dauke su ba.

Har ila yau a cikin garin Shinkafin, ‘yan bindiga sun kashe  wasu ‘yan kasuwa, Jamilu Jarma da wani wanda ake kira  Oke, suka kuma yi awon gaba da dukiyarsu a ranar Asabar zuwa wayewar garin Lahadi.

Mazauna garin Shinkafi sun koka a kan yadda ‘yan bindiga suka addabe su a ‘yan kwanakin nan, inda suke kai musu hare-hare  ba kakkautawa tun bayan da aka kammala zabukan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.