Isa ga babban shafi

An zargi wasu manyan jami'an Najeriya da jan kafa a binciken wasu kudaden mai

Majalisar wakilan Najeriya ta zargi Antoni Janar na kasar Abubakar Malami da ministan kudi Hajiya Zainab Ahmad kan kin baiwa majalisar hadin kan da ya dace a kokarin da take yi na binciken batan dala biliyan biyu da miliyan 400 na kudaden man fetur da aka sayar. 

Ministan sharia'ar Najeriya Abubakar Malami.
Ministan sharia'ar Najeriya Abubakar Malami. Daily Post
Talla

Tun farko dai an kafa kwamiti na musamman ne don zurfafa bincike game da batan wadannan kudade na akalla ganga miliyan 48 na danyen mai tun 2015. 

Sai dai kuma kwamitin ya zargi wadannan mutane da ke cikin wadana ake zargi da bijiro da wasu al’amurra da ke janyo jan kafa wajen aikin kwamitin. 

Wannan zargi na zuwa ne bayan da kwamitin ya sake gayyatar Antoni Janar Malami akan ya sake bayyana a gaban sa da kuma wasu takardu masu muhimmanci da zasu baiwa kwamitin damar ci gaba da binciken sa. 

Ko da yake bayan ranar laraba da aka sake zaman kwamitin, shugaban sa Mark Gbillah, ya ce abin takaici ne yadda masu ruwa da tsaki, suka ki baiwa kwamitin hadin kan da ya dace wajen gudanar da aikin sa. 

A cewar Gbillah, matukar aka ci gaba da tafiya a haka, tabbas kwamition bas hi da wni zabi illa amfani da karfi da yake da shi bisa doka wajen tilastwa masu ruwa da tsaki koma wadanda ake zargi ba da kai bori ya hau. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.