Isa ga babban shafi

Kotu a Birtaniya ta samu Ike Ekweremadu da laifin safarar sassan jikin mutum

Kotu a kasar Ingila, ta samu wani dan majalisar dattawan Najeriya Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice da laifin safarar sassan jikin mutum.

Kotun ta samu mutanen uku da laifin safarar wani matashi zuwa Biritaniya da nufin cire wani sassa na jikinsa bayan shari’ar da aka shafe makonni shida ana yi a Old Bailey.
Kotun ta samu mutanen uku da laifin safarar wani matashi zuwa Biritaniya da nufin cire wani sassa na jikinsa bayan shari’ar da aka shafe makonni shida ana yi a Old Bailey. AP
Talla

Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya tare da matarsa, da likitansu Obinna Obeta, an same su da laifin karya dokar bautarwa.

Kotun ta samu mutanen uku da laifin safarar wani matashi zuwa Biritaniya da nufin cire wani sassa na jikinsa bayan shari’ar da aka shafe makonni shida ana yi a Old Bailey.

Alkalin kotun ya gano cewa sun hada baki ne wajen daukar matashin mai shekara 21 wanda yake gudanar da sana’a a Legas zuwa Landan domin amfani da kodar sa.

Alkalin kotun mai shari’a Jeremy Johnson y ace zai yanke hukunci kan wannan tuhuma na da ‘yan kwanaki masu zuwa.

A watan Yunin 2022 ne, ‘yan sandan birnin Landan suka gurfanar da Beatrice Nwanneka mai shekaru 55, da Ike Ekweremadu, ‘dan shekaru 60 da haihuwa, a gaban Kotun Majistare ta Uxbridge.

A watan Fabrairun 2022, matashin mai shekaru 21, kotun ta ce an gabatar da shi ga wani sashin kula da lafiya mai zaman kansa a asibitin Royal Free da ke Landan a matsayin kani ga diyar Ekweremadu Sonia a kokarin da ya yi na shawo kan likitocin su yi dashen kodar ka kudi sama da yuro 80,000.

Davies ya ce Ekweremadu daya ne daga cikin ‘yan majalisar dokokin Najeriya da suka kaddamar da dokokin kasar kan yaki da safarar sassan jikin dan adam.

Ya ce Ekweremadu “ya amince ya ‘yarsa kodar wani, wanda ke cikin halin talauci kuma ya nisanta kansa da shi, wanda kuma ya yi amfani ne da mukamin sa na siyasa, bugu da kari kuma, ba ya son a tuntube shi kai tsaye game da halin da yaron ke ciki”.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.