Mutane 4 suka mutu a wata arangama tsakanin jami'an tsaro da 'yan Shi'a a Kaduna
Akalla mutane 4 ne ake zargin sun mutu a wata arangama tsakanin mabiya akidar Shi’a da kuma jami’an tsaron tawagar gwamnan jahar Kaduna da ke Najeriya Malam Nasiru El-Rufa’I a yankin Bakin Ruwa.
Wallafawa ranar:
Wani shaidar gani da ido ya shaidawa jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar cewar, anyi arangamar ne a lokacin da ‘yan Shi’an ke gudanar da tattaki, inda wasu daga cikin su suka fara yiwa tawagar gwamnan ihu da jifa da duwatsu lamarin da ya sanya jami’an tsaro yin harbi.
Daya daga cikin jagororin ‘yan shi’a a jahar Abdullahi Usman, ya ce wadanda aka kashe ba mambobin su bane face direbobin motocin haya.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jahar Kaduna DSP Mohammed Jalige ya tababtar da faruwar lamarin sai dai ya ce suna gudanar da bincike akai.
Wannan dai ba shine karo na farko da ake samun arangama tsakanin jami'an tsaro da mabiya akidar Shi'a a jahar Kaduna, domin ko a watan Disambar shekarar 2015 sai da aka samu rikici tsakanin sojoji da su a birnin Zaria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu