Isa ga babban shafi

Mutum hudu sun mutu a rikicin rashin Naira a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa rikici ya barke a sassan kasar, yayin da jama'a ke shan wahala wajen neman takardun kudi a bankuna, abin da ya haifar da asarar rayukan mutane akalla hudu a jihar Edo, kamar yadda jaridar Thenation ta ruwaito.

Masu zanga-zanga sun kuma kona tayoyi akan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna
Masu zanga-zanga sun kuma kona tayoyi akan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna © The Guardian Nigeria
Talla

Birane da dama daga kudancin kasar ne aka fi samun tarzoma saboda karancin takardun kudin, yayin da 'yan kasar ke zargin bankuna da hana jama'a kudade.

An rufe bankuna, yayin da masu sana'ar motar haya suka dakatar da zirga-zirga a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

A Warri da ke jihar Delta, fusatattun mutane sun cinnawa bankuna wuta, inda haka abin ya kasance a jihar Edo.

Haka zalika, an samu barkewar tarzoma a birnin Ibadan, yayin da al'umma da dama ke cigaba da bayyana fushin su, saboda karancin takardiun kudin.

Wannan dai na zuwa ne, yayin da kotun kolin kasar ta dage cigaba da ssauraron karar da wasu jihohi suka shigar gabanta, kan wa'adin ranar 10 ga watan fabrairu da CBN ta ayyana a matsayin ranar da zza a daina karbar tsoffin takardun kudi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.