Isa ga babban shafi

Boko Haram ta kashe malaman makaranta sama da dubu 2 a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce mayakan Boko Haram sun hallaka malaman makarantu 2,295 a jihohin Borno da Yobe da Adama tsakanin shekarar 2009 zuwa 2018, yayin da suka raba sama da dubu 19 daga muhallinsu. 

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Kwamandan Rundunar Tsaron NSCDC Ahmed Audi ya bayyana haka lokacin da yake kaddamar da wani sabon shirin samar da tsaro a makarantun Najeriya. 

Audi ya ce wadannan ‘yan ta’adda sun lalata makarantun da yawansu ya kai 1,500, tare da jikkata dalibai 1,280 tun daga shekarar 2014 kafin ayi nasarar dakile kaifinsu. 

Kwamandan ya ce wadannan munanan hare-hare sun yi matukar illa akan harkar koyarwa da kuma ci gaban kasa, abin da ya sa gwamnatin tarayya ta bullo da wannan sabon shiri na samar da tsaron da zai bai wa malamai da dalibai kariyar da suke bukata. 

Gwamnatin Najeriya ta dora alhakin samar da tsaro a makarantu akan rundunar tsaron ‘Civil Defence’ domin ganin an samar da yanayin da ake bukata na bai wa dalibai ilimi. 

Shugaban gwamnonin Najeriya Aminu Wazirin Tambuwal ya bayyana cewar daukacin jihohi 36 da ke kasar na shirye wajen hada kai da gwamnatin tarayya domin ganin na samu nasarar aikin. 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.