Isa ga babban shafi

Kotun Koli ta amince da Lawan a matsayin dan takarar Yobe

Kotun Kolin Najeriya ta amince da shugaban Majalisar Dokokin Kasar, Sanata Ahmed Lawan a matsayin halastaccen dan takarar kujerar Sanata karkashin jam’iyyar APC a mazabar Yobe ta Arewa, inda ta kwace tikitin takarar daga hannun Bashir Machina wanda a can baya, wata babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta amince da shi a matsayin halastaccen dan takara.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan Twitter/Nigerian Senate
Talla

A yayin jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Centus Nweze ya nuna rashin gamsuwa da matakain Bashir Machina na fara shigar da kara a babban kotun tarayya ta Damaturu wadda ta bai wa jam’iyyar APC da kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta INEC umarnin amincewa da shi a matsayin dan takarar kujerar sanata daga yankin Yobe ta Arewa.

A wancan lokacin, kotun da ta yi zamanta karkashin jagorancin Mai Shari’a Fadimatu Aminu, ta umarci APC da ta gabatar da sunan Machina ga hukumar INEC a matsayin wanda ya lashe zaben fid da gwanin da aka gudanar a ranar 28 ga watan Mayun bara.

Ita ma kotun daukaka kara da ke birnin Abuja, ta amince da hukuncin da kotun Damaturu ta yanke tare da kara tabbatar da Machina a matsayin halastaccen dan takarar jam’iyyar APC.

Lawan dai, ya sha kashi a zaben fid da gwani na dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC wanda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya lashe .

Koda yake, Lawan bai fafata a zaben fid da gwanin dan takarar sanata a mazabar Yobe ta Arewa ba, amma jam’iyyarsu ta APC ta aike da sunansa a matsayain dan takararta ga INEC , yayin da hukumar zaben ta ki amincewa da shi.

Machina da ya lashe zaben a hukumance, ya ki amincewa ya janye wa Lawan duk da matsin lambar da ya yi ta sha, inda har ya shigar da kara kotu domin neman a yi masa adalci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.