Isa ga babban shafi

NNPC na neman kariyar sojoji domin fara hako man fetur a Borno

Kamfanin Man NNPC a Najeriya ya nemi taimakon rundunar soji ta 7 da ke da cibiya a Maiduguri da ta taimaka masa wajen bai wa ma’aikatan da za su yi aikin hako mai a gabar Tafkin Chadi kariyar da ake bukata. 

Shugaban Kamfanin Mai na NNPC da ke Najeriya, Mele Kyari
Shugaban Kamfanin Mai na NNPC da ke Najeriya, Mele Kyari © Guardian
Talla

Manjo Janar Ali Nani mai ritaya, ya jagoranci tawagar wasu mutane 3 domin ganawa da kwamandan runduna ta 7, Manjo Janar Waidi Shuaibu domin gabatar da bukatar da kuma tattaunawa kan yadda za a samu biyan bukata. 

Sanarwar da kakakin rundunar ya gabatar, ta ce Janar Nani ya gabatar da bukatar ce a madadin kamfanin Didan wanda NNPC ya ba shi aikin hako man. 

Kwamandan runduna ta 7 Janar Shuaibu ya yi alkawarin bai wa ma’aikatan tsaron da suke bukata domin gudanar da ayyukansu. 

Janar Shuaibu ya ce rundunar za ta ci gaba da bada gudumawar da ta dace wajen kare lafiyar ma’aikatan da kuma kayan aikinsu, yayin da ake aikin sake gina yankin da rikicin Boko Haram ya shafa. 

A shekarun baya, irin wannan yunkuri na kamfanin man ya gamu da koma baya lokacin da mayakan Boko Haram suka kama wasu daga cikin ma’aikatan da ke aiki a yankin. 

Masana ma’adinai sun dade suna danganta Jihar Borno, musamman yankin Tafkin Chadi da arzikin man fetur da kuma iskar gas. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.