Isa ga babban shafi

Babbar mota dauke da sunduki ta kashe mutane 9 a Lagos bayan danne motar fasinja

Mutane tara ne aka tabbatar da mutuwar su, yayinda wata babbar mota da ke dauke da sunduki ta fada kan wata motar fasinja a jihar Lagos da ke tarayyar Najeriya. 

Wasu motocin Sunduki.
Wasu motocin Sunduki. AFP - STR
Talla

Al’amarin dai ya faru ne a yankin Ojuelegba da ranar Lahadin nan a lokacin da motar bas din ta tsaya don daukar fasinja a kasan gada, inda sundukin mai tsawon kafa 20 a subuce ya fada wa motar. 

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewar motar bas din da kontenan ta fadawa cike ta ke fasinja, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwa da kuma raunata wasu da dama. 

A lokacin da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jahar Lagos Dr. Femi Oke-Osanyintolu, ya ce daga cikin wadanda suka rasa rayukan su akai maza 4 da mata 3 da yara 2 sai kuma wata mata da aka kubutar da ranta. 

Ya ce binciken farko da suka gudanar ya nuna cewar, babbar motar ta kwace wa matukin ta ne inda sundukin da ta ke dauke da shi ya fita ya fadawa bas din da ke tsaye a gefen gadar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.