Isa ga babban shafi

Kwara za ta dauki sabbin malaman makaranta 600 don bunkasa ilimi a jihar

Gwamnatin jihar Kwara a Najeriya ta sanar da shirin daukar sabbin malaman makaranta akalla  600 aiki don maye gurbin wadanda ko dai suka mutu ko kuma suka yi ritaya a wani yunkuri na bunkasa harkar koyo da koyarwa a jihar.

Wani Malami lokacin da ya ke koyar da dalibinsa.
Wani Malami lokacin da ya ke koyar da dalibinsa. artuz.jpg
Talla

Hukumar kula ilimin bai daya ta jihar ta bayyana cewa akwai tarin guraben malamai a jihar wanda rashinsu ya haddasa koma baya ga ilimi dalilin daya sanya bude fagen daukar sabbin ma’aikatan don cike gibin.

Shugaban hukumar Farfesa aheem Adaramaja a wani jawabinsa gaban manema labarai ya ce dukkanin wadanda ke da shaidar kwarewar koyarwa na da damar neman wannan aiki.

Najeriya dai na sahun kasashen da kef ama da matsalar koma bayan Ilimi musamman ta yadda gwamnatoci suka yi biris wajen daukar kwararrun malamai don tafiyar da harkokin koyarwa a makarantu mallakin gwamnati.

Kazalika kasar na sahun yankunan da kef ama da tarin marasa aikin yi galibi wadanda suka yi karatu dalilin da ke sanya ficewar kwararru daga kasar don samun kyakkyawar rayuwa a ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.