Isa ga babban shafi

Boko Haram sun kashe makiyaya da dama a Borno

Bayanai daga jihar Borno da ke tarayyar Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 17, bayan da mayakan Boko Haram suka kai masu farmaki domin sace dabbobinsu.

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP wanda ya ruwaito wannan labari, ya ce mayakan na Boko Haram sun kai harin ne a kan wasu makiyaya kusa da kauyen Airamne da ke karamar hukumar Mafa a jihar Borno, to sai dai makiyayen sun nuna tirjiya har aka yi dauki ba-dadi a tsakanin bangarorin biyu.

Wani jami’in tsaron sa-kai da bayyana sunansa a matsayin Babkura Kolo, ya ce bayan wannan artabu an gano gawarwakin makiyaya 17, yayin da maharan suka yi awun gaba da dabbobi masu tarin yawa.

Wadanda suka tsira da rayukansu sun bayyana cewa mayakan na Boko Haram sun zo ne masu tarin yawa dauke da manyan makamai, lamarin da ya sa suka fi karfin makiyayen duk da cewa su ma sun mallaki domin kare kansu.

Ga alama dai mayakan na Boko Haram na da babban sansaninsu ne a wani gandun daji da ake kira Gajiganna wanda ya hade da gandun dajin Sambisa da ke matsayin mabbar maboyar masu da’awar jihadi a yankin Arewa masu gabashin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.