Isa ga babban shafi

An aike da dalibin da yace A'isha Buhari ta yi 'bulbul gidan yari

Yanzu haka dai kotu a Najeriya, ta aike da dalibin nan da ake zargin 'uwargidan shugaban kasar Aisha Buhari ta bada umarnin a lakada masa duka gidan yari, kafin a ci gaba da yi masa shari'a.

uwargidan shugaban Najeriya, A'isha Buhari
uwargidan shugaban Najeriya, A'isha Buhari TWITTER/AISHA M. BUHARI
Talla

Kungiyoyin Kare Hakkin Bil'adama a ciki da wajen Najeriya nae ci gaba da bayyana rashin jin dadinsu kan cin zarafin dalibin da ke karatu a jami'ar Jigawa tare da lakada masa duka.

Hajiya Naja'atu Mohammed, Kwamishiniya a Hukumar 'Yan sandan Kasar ta ce, ya kamata a kama 'uwargidan shugaban kasar saboda ta keta doka.

Hajiya Naja'atu ta bayyana haka ne a wata hira da ta yi da sashen Hausa na RFI, inda take cewa, babu dokar da ta bai wa uwargidan shugaban kama wani tare da tsare shi.

Rahotanni na cewa, uwargidan shugaban ce ta bai wa jami'an tsaro umarnin dauko mata Aminu Adamu daga jami'ar ta Jigawa bayan ya wallafa wasu kalamai a kanta, inda yake cewa, "Su mama an ci kudin talakawa an koshi".

A ranar Laraba aka gurfanar da dalibin a gaban kotu da ke birnin Abuja, yayin da jama'a da dama daga sassan Najeriya ke ci gaba da bai wa A'isha Buhari hakuri kan abin da matashin ya yi mata.

Kungiyar Daliban Najeriya ita ta tsoma baki cikin lamarin, tana mai bukatar uwargidan shugaban kasar da ta gaggauta sakin sa.

A makon gobe ne dalibin zai fara zama jarrabawar kammala ajin karshe a jami'ar da yake karantar fannin ilimin kula da tsaftar muhalli.

Su ma dai iyayen yaron sun roki A'isha da ta yi wa Allah ta yafe wa dansu kan laifin da ya yi mata, musamman idan ta yi lakari da matsayinta na cewa, ita uwa ce ga kowa a cewarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.