Isa ga babban shafi

Rashin man fetur na kara kamari a Najeriya duk da ikirarin gwamnati

Gwamnatin Najeriya da ‘yan kasuwar man fetur sun bayar da bayanai mabambanta kan matsalar karancin man fetur da ta addabi jihohin kasar tsawon makwanni.

Layin masu neman Man Fetur a Najeriya
Layin masu neman Man Fetur a Najeriya Nigerian Leadership
Talla

Yayin da NNPC ta ce layukan da ake samu a Legas da Abuja ya fi yawa saboda "ayyukan samar da ababen more rayuwa" da ake yi a kewayen Apapa da kuma kalubalen hanyoyin da ake fuskanta a wasu sassan Legas, ita kuwa kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta ce ya samo asali ne sakamakon tsadar farashin da masu gidajen man fetur suka sanya a ciki.

A cikin makonnin da suka gabata, an samu dogayen layuka a gidajen mai dake garuruwa da dama a fadin kasar, lamarin da ya sa jama’a ke kokawa wajen zuwa aiki ko kuma yin wasu harkokin yau da kullum.

Karancin man ya ci gaba da kasancewa a gidajen mai, duk da ikirarin da gwamnati ta yi na cewa tana da isasshen mai.

A watan Oktoba, karancin man fetur ya afkawa manyan biranen Najeriya da suka hada da Abuja da Legas. A wancan lokacin, said ai hukumar kula da man fetur ta Najeriya  ta dora alhakin karancin man fetur da ambaliyar ruwa da aka samu a Lokoja, babban birnin Jihar Kogi, wanda ya hana manyan motocin dakon man fetur rarraba shi.

Da dama daga cikin gidajen mai a APO, Wuse, Gwagwalada da Banex da ke Abuja, babban birnin kasar ana sayar da man fetur ne akan naira 179 zuwa 210. A wajen Abuja kuma mutane sun tabbatar da cewa gidajen mai suna sayar da man akan naira 250 kan kowacce lita.

Bayanai daga Abuja na cewa har yanzu ana samun dogon layi a gidajen sayar da man fetur da ke sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.