Isa ga babban shafi

Gwamnatin Kano ta haramta zirga-zirgar Adaidaita Sahu

Gwamnatin Kano ta Najeriya ta haramta zirga-zirgar babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidaita Sahu a wasu manyan hanyoyin da ke jihar, kuma daga gobe Laraba ne wannan doka za ta fara aiki.

Gwamnatin Kano ta haramta zirga-zirgar Adaidaita Sahu
Gwamnatin Kano ta haramta zirga-zirgar Adaidaita Sahu © LegitHausa
Talla

A jiya Talata ne Jami’in Yada Labaran Hukumar Kula da Zirga-zirzgar Ababen Hawa ta Jihar, KAROTA, Nabilusi Na’isa, ya fitar da wata sanarwa da ke magana game da haramcin.

Sanarwar ta ce, gwammatin jihar ta dauki matakin ne bayan ta fara samar da manyan motocin bas-bas guda 100 na zamani da kuma motocin tasi guda 50 wadanda za su ci gaba da jigilar fasinjoji a kan hanyoyin da aka haramta zirga-zirgar Adaidata Sahun.

Daga cikin hanyoyin da dokar ta shafa, har da hanyar Ahmadu Bello, daura da Mundubawa zuwa Gazawa da Tal’udu da Gwarzo.

Sanarwar ta ce, nan gaba kadan, za a sake bayyana haramccin zirzga-zirgar Adaidaita Sahun a wasu  Karin hanyoyin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.