Isa ga babban shafi

Matsalar karancin mai ta ta'azzara a Lagos

Matsalar karancin man fetur ta karade sassan birnin Lagos da ke kudancin Najeriya, yayin da al’umma ke nuna damuwa kan musabbabin karancin duk da cewa,  ‘yan kasuwa masu zaman kansu na sayar da lita guda sama da Naira 210.

Daidaikun gidajen mai ne ke sayar da fetur a jihar Lagos
Daidaikun gidajen mai ne ke sayar da fetur a jihar Lagos irinnews
Talla

A halin yanzu, daidaikun gidajen mai ne ke sayar da fetur din a sassan jihar ta Lagos, yayin da dama ke ci gaba da kasancewa a rufe.

Wakilan RFI Hausa sun bada rahoton yadda motoci da babura suka yi dogayen layuka a kokarinsu na ganin sun sayi man.

Wasu daga cikin gidajen man na sayar da lita guda akan farashin Naira 210 ko 215 zuwa 220, sabanin farashin da gwamnati ta kayyade na Naira 169 zuwa 170.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.