Isa ga babban shafi

Shugaba Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudin Naira

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudin kasar da aka sauyawa fasali wadanda suka kunshi Naira 200 da 500 da kuma 1000 gabanin fitar da su ga jama'a a ranar 15 ga watan gobe na disamba.

Sabbin kudaden Najeriya.
Sabbin kudaden Najeriya. © Bashir Ahmad
Talla

Gwamnan babban bankin Najeriyar CBN Godwin Emefiele ne ya gabatar da sabbin takardun ga shugaba Muhammadu Buhari yau laraba a fadarsa ta Villa da ke Abuja babban birnin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa, an gabatar da sabbin takardun kudin ga zaman majalisar zartaswa na yau gaban tarin 'yan majalisa da ke wakiltar sassan kasar.

A ranar 15 ga watan da Disamba mai zuwa ne ake saran fara amfani da sabbin takardun kudin na Naira gabanin fara janye tsaffin kudin da ake amfani da su a yanzu zuwa nan da karshen watan Janairun 2023.

Gwamnan bankin na CBN ya roki al'ummar Najeriya da su gaggauta mika tsaffin kudaden da ke hannunsu ga bankuna mafi kusa da su don samun nasarar iya kammala janye kudin nan da ranar 31 ga watan na Janairun 2023.

Ana saran dai sauya fasalin kudin na Naira ya taimaka wajen daga darajar takardar kudin wadda ta gamu da mummunan koma baya a shekarun baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.