Isa ga babban shafi

Kalubalen karuwar yawan jama'a ga al'ummar Lagos ta Najeriya

Yawan al’ummar duniya na ci gaba da karuwa cikin sauri fiyeda yadda majalisar dilkin duniya ta kiyasta, domin a shekarar 2011 majalisar ta yi kiyasin cewar sai nan da shekarar 2030 ne yawan al’ummar duniya zai kai biliyan 8, sai dai a cikin shekaru 11 kadai an cimma wancan adadi.

Wani yanki a Jihar Lagos ta kudancin Najeriya.
Wani yanki a Jihar Lagos ta kudancin Najeriya. AFP - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Jahar Lagos da ke tarayyar Najeriya na daya daga cikin biranen da aka fi samun karuwar al’umma, ganin yadda daga shekarar da ta gaba zuwa yanzu an samu karuwar kusan kashi 4 na al’ummar da ke rayuwa a cikin ta, lamarin da ake hasashen ya kawo adadin al’ummar jahar zuwa miliyan 28 kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana, duk da ya ke wasu na ganin adadin iya zarce haka.

Toh ko ya ya yawan ke shafar rayuwar al’ummar wannan birnin? Khamis Saleh ya hada mana rahoto a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.