Isa ga babban shafi

Boko Haram ta kashe wasu mata da ta ce mayu ne

Mayakan Boko Haram sun kashe wasu mata a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya bayan sun zarge su da maita tare da lashe kurwar ‘ya’yan daya daga cikin kwamandojin mayakan.

Wasu mayakan kungiyar Boko Haram
Wasu mayakan kungiyar Boko Haram Defencepost
Talla

A makon jiya ne, Boko Haram ta tsare mata 40 a kusa da kauyen Gwoza bayan kwamandan mayakan, Ali Guyile ya bada umarnin haka jim kadan da mutuwar ‘ya’yansa da ya ce, mayun ne suka lashe kurwarsu kamar yadda wata mata da ta tsira ta shaida wa manema labarai.

Kwamandan na Boko Haram mai shekaru 35, ya bai wa mayakansa umarnin gadin duk wani gida da ake zargin akwai mayya a cikinsa, kafin daga bisani ya yi wa wasu daga cikinsu kisan gilla ta hanyar yankar rago.

Matar da ta tsira ta ce, tuni ta nemi mafaka a birnin Maiduguri bayan ta kubuta daga hannun mayakan kuma a cewarta, mata 14 ne suka kashe a ranar Alhamis da ta gabata  bisa zargin su da maitar.

Sannan kwamandan ya ce, zai ci gaba da gudanar da bincike domin zakulo karin matan da ke da hannu a mutuwar ‘ya’yan nasa kamar yadda matar da shaida.

Gwamnatin jihar Borno ta ce, tana gudanar da bincike a bangarenta game da wannan al’amari.

Zargin maita ba wani sabon al’amari ba ne a Najeriya, kasar da ke da mabanbantan addinai,  akasari, Musulunci da Kiristanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.