Isa ga babban shafi

Dakarun Najeriya sun kashe manyan kwamandojin ISWAP a Borno

Wani hari da sojojin sama na Najeriya suka kai kan maboyar mayakan ISWAP da ke Belowa a karamar hukumar Abadam a jihar Borno ya  hallaka wasu manyan Kwamnadojin Kungiyar ISWAP da wasu mayakansu da dama.

Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya. © Afolabi Sotunde/Reuters
Talla

Wannan na daga cikin nasarorin da ake samu  a yaki da ta’addanci a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotanni daga yankin sun ce an kashe Ali Kwaya da Bukar Mainoka, wadanda manyan kwamandoji ne a kungiyar ISWAP, da sauran mayakan kungiyar, sakamakon harin da aka kai musu ta sama.

Wata majiyar soji ta ce runduna ta musamman ta Operation Hadin Kai ce ta kai wannan hari a yankin Belowa a ranar 5 ga watan Nuwamban nan.

Belowa  na daga cikin yankuna kalilan da kungiyar ISWAP da Boko Haram suka saura a karamar hukumar Abadam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.