Isa ga babban shafi

Sama da 'yan gudun hijira 200,000 ne ke cikin yunwa a Najeriya - HRW

Sama da ‘yan Najeriya 200,000 da aka raba da muhallansu sakamakon tashin hankalin da aka dade ana fama da shi ne suke kokawa yanzu haka, saboda rashin abinci da matsuguni bayan da hukumomi a yankin arewa maso gabas suka rufe wasu sansanonin da suke zaune tare da dakatar da agaji, inji kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa wato Human Rights Watch.

Sansanin 'yan gudun hijira na Jere da ke garin Maiduguri a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Sansanin 'yan gudun hijira na Jere da ke garin Maiduguri a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya. AP - Chinedu Asadu
Talla

A watan Oktoban 2021, jihar Borno, wato inda rikicin Boko Haram yafi kamari, ta sanar da cewa ta rufe dukkan sansanonin da ke rike da dubban mutanen da suka rasa matsugunansu tare da mayar da wasu daga cikinsu zuwa yankunansu.

Gwamnatin jihar dai ta tabbatar da cewa an samu cikakken tsaro, don haka ya kamata a yaye mutanen da suka rasa matsugunansu daga tallafin jin kai.

A wani rahoto da ta fitar ranar Laraba, kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce mutanen da aka kora daga sansanonin na kokawa kan rashin biyan bukatunsu na yau da kullun da suka hada da abinci da matsuguni a wuraren da suka koma ko kuma aka sake tsugunar da su.

Sama da mutane 140,000 ne aka kwashe daga sansanoni takwas dake jihar Borno yayin da aka dakatar da tallafin abinci ga wasu sansanoni biyu a watan Agustan wannan shekara, inji Human Rights Watch. Wadannan sansanonin biyu suna dauke da mutane sama da 74,000 kuma an tabbatar da cewa za a rufe su a karshen wannan shekara.

“Gwamnatin jihar Borno tana kuntawa dubban mutanen da suka rasa matsugunansu, wadanda ke rayuwa cikin mawuyacin hali, domin cimma wata manufa ta ci gaban gwamnati na kawar da mutane daga ayyukan jin kai,” in ji wakiliyar Human Rights Watch a Najeriya, Anietie Ewang.

"Ta hanyar tilasta wa mutane ficewa daga sansanonin ba tare da samar musu hanyoyin da za su iya samun tallafi ba, gwamnati na kara ta'azzara wahalhalun da suke ciki tare da kara musu rauni," in ji ta.

Ko menene martanin gwamnati?

Kwamishinan yada labarai na jihar Borno Babakura Abba Jato ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ba zai iya cewa komai ba kan wannan rahoton.

Gwamnatin jihar ta ce wasu yankunan da mayakan Boko Haram suka mamaye a baya an samu kwanciyar hankali don 'yan yankin su koma, kuma ta sake inganta tsaro a asu kauyuka, ko da yake kungiyoyin agaji sun ce har yanzu suna fuskantar hare-hare.

Wasu daga cikin sansanonin da mutanen da suka rasa matsugunansu sun fuskanci barkewar cutar kwalara, kuma kananan yara ne suka fi fama da cutar.

A watan da ya gabata, kimanin mutane 2,000 ne suka fara kaura zuwa wani sabon rukunin gidaje a Ngarannam wanda Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin jihar suka sake ginawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.