Isa ga babban shafi

Shugaba Buhari ya tafi duba lafiyarsa a Birtaniya

A yau ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi balaguro zuwa kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya tashi daga Abuja zuwa Glasgow da Paris
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya tashi daga Abuja zuwa Glasgow da Paris © Nigeria presidency
Talla

Mai ba shugaban kasar shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya ce shugaban zai dawo kasar ne a mako na biyu na watan Nuwamba.

Shugaban wanda ya koma kasara ranar Juma’ar da ta gabata daga ziyarar aiki ta kwanaki shida a birnin Seoul, babban birnin kasar Koriya ta Kudu, ya tafi kasar Birtaniya ne bayan ya jagoranci wani taron gaggawa na kwamitin tsaron kasa a fadar gwamnati da ke Abuja.

Taron da aka yi a fadar shugaban kasar tare da shugabannin tsaro an kira shi ne domin kara nazari da karfafa hanyoyin samar da tsaro a kasar.

Buhari, ya ce batun tafiyar tasa bata da nasaba da rahoton da ake cewa za a kai hare-hare a babban birnin kasar Abuja, ya kara da cewa ya kamata jama’ar kasar su kwantar da hankulansu, saboda jami’an tsaro na cikin shirin ko ta kwana, tun bayan harin da aka kai gidan yari Kuje a watan Yuli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.