Isa ga babban shafi

APC: Kotu a Najeriya ta rusa zaben takarar gwamnan jihar Adamawa

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Yola ta soke zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka tsayar da Sanata Aishatu Binani a matsayin ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa.

Aishatu Binani
Aishatu Binani © daily trust
Talla

A wani hukunci na sama da sa’o’i uku da mai shari’a Abdulaziz Anka ya zartar a ranar Juma’a, kotun ta bayyana cewa an yanke hukuncin ne bisa wasu kwararan hujjoji na rashin bin ka’idojin jam’iyya da na kundin tsarin mulkin Najeriya, wajen gudanar da zaben fidda gwanin.

Nuhu Ribadu, wanda ya zo na biyu a yayin zaben, ya maka Binani, APC, da INEC gaban babbar kotu, yana neman a soke zaben fidda gwanin da aka gudanar a ranar 27 ga watan Mayun 2022.

Ya nemi a haramtawa Sanata Binani tsayawa takara a kan zargin sayen kuri’u da kuma jerin sunayen wakilai ba bisa ka’ida ba daga karamar hukumar Lamurde ta jihar.

A cewarsa, a zaben fidda gwanin anyi aringizon kuri’u, sakamakon fitar da ‘yan takara daga majalisar Lamurde kuma babu sunayen wakilan da suka fito daga yankin.

Kotun ta bayyana cewa babu dan takarar jam’iyyar APC a jihar a zaben 2023 amma ta ce mai kara da wadanda ake kara suna da damar daukaka kara kan hukuncin.

A nasu martanin lauyoyin Nuhu Ribadu da Sanata Binani sun yi alkawarin yin nazari kan hukuncin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.