Dakarun Najeriya sun kashe kasurgumin dan ta'adda da mabiyansa 30 a Kaduna
Rahotanni daga jihar Kaduna a Najeriya sun ce sojoji sun samu nasarar kashe Ali Dogo, daya daga cikin kasurguman ‘yan ta’addan da suka addabi jama’a da satar mutane.
Wallafawa ranar:
Wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaya sunanta da kafar watsa labaran PRNigeria ta ruwaito, ta ce an kashe Ali Dogo tare wasu ‘yan ta’addan akalla 30 ne a yayin ruwan wutar da jiragen yakin Najeriya suka yi wa sansanoninsu a wani yanki na karamar hukumar Giwa .
A ‘yan kwanakin baya bayan nan ne dai kasurgumin dan fashin dajin, ya tsere daga maboyarsa da ke jihar Neja zuwa yankin na Giwa a Kaduna, sakamakon hare-hare babu kakkautawa da jiragen yakin suka kaddamar kansa.
Cikin makon da ya gabata, wani rahoton masu bibiyar lamurran tsaro a Najeriya, ya ce an samu raguwar satar mutane a kasar da kashi 28 cikin 100 a watan Agustan da ya gabata na shekarar 2022, idan aka kwatanta da abinda aka gani a cikin watan Yulin da ya gabace shi.
Rahoton ya alakanta raguwar matsalar tsaron da aka samu da hare-haren da sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro suka kaddamar ba kakkautawa kan sansanonin miyagun a sassan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu