Isa ga babban shafi

Najeriya: Kayayyakin biliyoyin Naira na ci gaba da rubewa a tashohin jiragen ruwa

A Najeriya, bincike ya nuna cewa sama da kaya 8,000 ne da kudinsu ya kai kimanin Naira Tiriliyan 3, a halin suka makale a manyan tashoshin ruwan kasar guda uku wato Apapa, Tin Can da kuma Onne ba tare da wani kokari ko kadan ba wajen ganin an samar da dawwamammen maslaha a kan tabarbarewar da tarkacen ya haifar.

Kwantenar kaya sun mamaye kusan kashi 25 na tashar jiragen ruwan a Najeriya.
Kwantenar kaya sun mamaye kusan kashi 25 na tashar jiragen ruwan a Najeriya. © guardian
Talla

Bincike ya nuna cewa an yi watsi da fiye da kwantena 2,000 a tashar jiragen ruwa ta Onne, yayin da 6,000 ke makale a tashar jiragen ruwan Tin Can da Apapa na Legas.

Abin da ake ganin masu shigo da kaya sun watsar da su bayan da jami’an hukumar kwastam ta Najeriya suka tsare kayan.

Kwantenar kaya sun mamaye kusan kashi 25 na tashar jiragen ruwan kasar.

Doka ta baiwa hukumar kwastam damar yin gwanjon kayayyakin da suka kai kwanaki 90 da isowa tashar jirgin ruwa ba a kashe su ba.

Sai dai an kwashe akalla shekaru uku wadannan kayayyakin na jibge a tashoshin jiragen ruwa amma har yanzu ba a yi gwanjon su ba.

Sama da shekara guda da hukumar kwastam ta zuba biliyoyin Naira wajen siyan na’urorin daukar hoto na lantarki don gudanar da jarabawar daukar kaya a tashar jiragen ruwa, amma har yanzu hukumar ba ta sanya na’urar daukar hoton ba.

Duk da daukar sabbin na’urorin daukar hoto a watan Satumbar 2021, tashoshin jiragen ruwa na Tin Can da Onne, da kuma kan iyakar Seme, har yanzu sun dogara da gwajin da ake yiwa kayan da suka shiga a baya, inda jami’an Kwastam suka yi korafin cewa ana daukar sama da sa’o’i biyar kafin a tantance kwantena daya, wanda hakan ya haifar da tsaiko ga wadanda aka sayo. .

Legas na da tashar jiragen ruwa mafi girma a Afirka ta Yamma, inda yawan kayan da aka shigar da su kasar a wasu lokutan ya kan kai sama da 6,000, wanda idan aka kididdige su kan kai kimanin Naira tiriliyan uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.