Isa ga babban shafi

Najeriya: NDLEA ta kona hodar ibilis ta sama da biliyan 195 a Legas

Hukumar NDLEA dake yaki da mu’amala da miyagun kwayoyi a Najeriya, ta kona kusan tan 2 na hodar ibilis ranar Talata, wanda ta kama a wani gidan aje kayayyaki dake Ikorodu, a birnin Legas.

Yadda jami'an hukumar NDLEA suka kona kusan tan biyu na hodar ibilis da aka kame a jihar Legas
Yadda jami'an hukumar NDLEA suka kona kusan tan biyu na hodar ibilis da aka kame a jihar Legas © rfi
Talla

Shugaban Hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya ne, ya jagoranci bikin kona hodar ibilis din da aka gano a wani gini dake Ikorodu tare da kama wasu mutane guda 5, cikin su harda wani dan kasar Jamaica.

Kona hodar ibilis din ya biyo bayan samun umurnin kotun Lagos, wadda ta baiwa Hukumar damar kona ta a bainar jama’a.

Shugaban Hukumar Janar Buba Marwa ya bayyana kudin hodar da aka kona akan Dala miliyan 278 da dubu 250 ko, kwatnkwacin kudin kasar naira biliyan 194 da miliyan 775.

Marwa ya koka akan yadda ake shigar da kwayar cikin Najeriya, yayin da yayi alkawarin ci gaba da jajircewar Hukumar NDLEA, wajen dakile masu aikata wadannan laifuffuka.

Shugaban da ya samu wakilcin Daraktan gurfanar da masu laifi a gaban kotu, Sunday Joseph, yace daga ranar 25 ga watan Janairu zuwa yanzu, Hukumar ta samu gagarumar nasara wajen gabatar da masu safarar kwayar da kotu ta daure wadanda yawansu ya kai 2,904, yayin da ake ci gaba da shari’ar wasu.

Marwa yace nasarar da suka samu a Ikorodu ya tabbatar da cewar masu zuba jari akan wannan mummunar sana’ar, zasu ci gaba da tafka asarar, yayin da NDLEA zata ci gaba da kama su tana tsarewa.

Shugaban ya yabawa abokan aikin su irin su Hukumar yaki da safarar kwayoyi ta Amurka, da ta taimaka musu wajen samun nasara, tare da rundunar sojin Najeriya.

Mai Magana da yawun Hukumar Femi Babafemi yace Marwa ya bukaci taimakon 'yan Najeriya wajen ci gaba da samun nasarar murkushe masu safarar kwayoyin dake bata rayuwar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.