Isa ga babban shafi

Malaman jami'a sun kara tsawaita yajin aiki a Najeriya

Kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta yanke shawarar ci gaba da yajin aikin da ta shafe rabin shekara  tana yi, bayan jerin tataunawa da aka shafe lokaci ana yi tsakaninta da  wakilan gwamnatin Najeriya,.

Wani taron kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU da Ministan Kwadagon Najeriya Chris Ngige.
Wani taron kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU da Ministan Kwadagon Najeriya Chris Ngige. © Daily Trust
Talla

ASUU ta yanke wannan shawarar ne  bayan taron kwamitin gudanarwa na kungiyar a shelkwatar kungiyar da ke jami’ar Abuja da safiyar Litinin din nan, inda malaman suka tafka muhawwara mai zafi a tsakaninsu.

A waje daya kuma, jaridar Punch da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito kakakin ma’aikatar ilimi ta gwamnatin kasar, Ben Goong na bayanin cewa gwamnati ta dauki dukkannin matakan da suka dace don ganin an kawo karshen yajin aikin.

A game da matakan da za a dauka a nan gaba, Goong ya ce gwamnati ta riga ta kaddamar da kwamitin da zai yi aikin hade tsarin biyan albashin ma’aikata na bai daya wato IPPIS da UTAS da UP3, yana mai cewa hakan zai tabbatar da cewa gwamnatin ta yi amfani da guda daga cikinsu wajen biyan albashi.

A ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar ne kungiyar ASUU ta ayyana fara wani yajin aiki bayan taron da ta gudanar a jami’ar Lagos da ke kudu maso yammacin kasar.

Babu wata sanarwa a hukumance daga kungiyar ASUU a game da dalilin tsawaita wannan yajin aiki da ya shiga kwana ta 196.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.