Isa ga babban shafi

Rundunar Sojin Najeriya ta kori sojojinta 2 da suka kashe Sheikh Goni Aisami

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da tube jami’anta 2 da suka kunshi John Gabriel da Gidon Adamu wadanda aka samu da laifin kisan fitaccen malamin addinin Islama a jihar Yobe Sheikh Gwani Aisami.

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor, yayin ganawa da wasu daga cikin dakarun kasar.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor, yayin ganawa da wasu daga cikin dakarun kasar. AP - Jossy Ola
Talla

Rundunar Sojin Najeriyar ta sanar da wannan mataki ne a wani taron manema labarai da ta kira karkashin bataliya ta 241 RECCE da jami’an biyu ke aiki karkashinta a garin Nguru da ke jihar ta Yobe.

Mukaddashin babban kwamandan bataliya ta 241 ta rundunar sojin Najeriya ta RECCE, Laftanal kanal I O Sabo ya shaidawa manema labarai cewa abin da sojojin biyu suka aikata ba da shi ne za a yiwa rundunar Sojin gabaki dayanta kudin goro ba.

A cewar kwamanda bayan tube jami’an biyu, sun mika su ga jami’an ‘yan sanda don amsa tuhuma kana bin da suka aikata tare da gurfanar da su gaban kotu don fuskantar shari’a.

Guda cikin korarrun Sojojin biyu Mr Gabriel, tuni ya amsa laifin kisan malamin addinin a ranar 19 ga watan da muke ciki na Agusta, lokacin da tubabben Sojan ya nemi sace motar malamin bayan ya rage mishi hanya daga shingen binciken da ya ke aiki.

Kisan na Sheikh Aisami dai ta tayar da hankalin al'ummar Najeriya inda ake ci gaba da kiraye-kirayen ganin an tabbatar da adalci wajen hukunta wadanda ake tuhuma da kisan, cikin masu kiraye-kirayen kuwa har da manya-manyan malaman addini da ke da karfin fada aji baya ga shugaba Muhammadu Buhari wanda shi kansa ya ce ba za a lamunci irin laifukan daga Soji ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.