Isa ga babban shafi

Najeriya: Har yanzu tsugune ba ta kare ba game da daukar sabbin 'Yan sanda

An samu takun-saka tsakanin hukumomin ‘yan sandan Najeriya, dangane da daukar sabbin jami'an ‘yan sanda 10,000 aiki.

Nigeria Police Force
Nigeria Police Force Nigeria Police Force
Talla

Hukumar ‘yan sandan Najeriya a makon da ya gabata ne ta sanar da cewa, da zarar an kammala daukar sabbin ma’aikata na shekarar 2020, zata fara shirin tantance na shekarar 2021.

Amma Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar Usman Alkali Baba, a karshen mako ya yi kira ga masu neman shiga aikin na shekarar baran da su fara dakon guraben da za a fitar.

A shekarar 2018 ne shugaban kasar Muhammadu Buhari ya amince da daukar sabbin jami’an ‘yan sanda 60,000 na tsawon shekaru shida.

Shirin daukar ma'aikata na 2020, duk da haka, ya shiga cikin rudani bayan da hukumomin 'yan sandan suka nace cewa suna da hurumin daukar 'yan sanda aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.