Isa ga babban shafi

Sojoji sun kwace gari na karshe daga hannun Boko Haram a Borno

Rundunar sojin Najeriya ta kwace gari na karshe wato Guduumbale da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar daga hannun mayakan Boko Haram.

Wasu daga cikin sojojin Najeriya masu fada da 'yan ta'adda a Borno
Wasu daga cikin sojojin Najeriya masu fada da 'yan ta'adda a Borno STEFAN HEUNIS/AFP
Talla

Bisa bayanan da sashen Hausa na RFI ya tattara, ya gano cewa har yanzu wannan gari babu kowa a cikinsa face sojoji, sai kuma daidaikun Fulani da dabbobinsu.

Musa Ibrahim da ya bi ayarin gwamnatin jihar Borno zuwa wannan gari, ya yi mana karin bayan kan abin da idansa ya gane masa.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren bayanin Ibrahim.

Akalla mutane dubu 40 ne suka rasa rayukansu a yankin arewa maso gabashin Najeriya, yayin da kimanin miliyan biyu suka tsere daga muhallansu tun daga shekarar 2009 sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram.

Rikicin na Boko Haram ya yadu zuwa kasashe makwabta da suka hada da Chadi da Kamaru da Nijar, lamarin da ya jefa al’ummar yankin Tafkin Chadi cikin garari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.