Isa ga babban shafi

An kashe ma'aikatan agaji 35 a arewacin Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a kare lafiyar ma’aikatan agaji da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda mayakan jihadi suka kashe 35 daga cikin masu aikin agajin a cikin shekaru shida da suka gabata.

Wasu ma'aikatan Kungiyar Agaji ta Red Cross a yayin kai dauki lokacin aukuwar wani hari a birnin Maiduguri na jihar Borno a Najeriya.
Wasu ma'aikatan Kungiyar Agaji ta Red Cross a yayin kai dauki lokacin aukuwar wani hari a birnin Maiduguri na jihar Borno a Najeriya. © vanguard
Talla

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce, wasu alkaluma sun nuna cewa, an kuma raunata ma’aikatan agajin 22, sannan aka yi garkuwa da 28 tun daga shekara ta 2016.

Akalla mutane dubu 40 ne suka rasa rayukansu a yankin arewa maso gabashin Najeriya, yayin da kimanin miliyan biyu suka tsere daga muhallansu tun daga shekarar 2009 sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram.

Rikicin na Boko Haram ya yadu zuwa kasashe makwabta da suka hada da Chadi da Kamaru da Nijar, lamarin da ya jefa al’ummar yankin Tafkin Chadi cikin garari.

Majalisar Dinkin Duniya ta jinjina wa ma’aikatan agaji kan yadda suke kai dauki na ceton-rai ga miliyoyin al’ummar yankin mai fama da tashin hankali.

A wannan shekarar kadai, mutane miliyan 8.4 ke cikin bukatar agaji a yankin arewa maso gabashin Najeriya kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.