Isa ga babban shafi

Tsoffin 'Yan Boko Haram za su fara aikin share titunan Maiduguri

Gwamnatin jihar Borno da ke Najeriya, ta bullo da wani shiri na bai wa tsoffin mayakan Boko Haram aikin share hanyoyin birnin Maiduguri, a wani mataki na sake mayar da su cikin al’umma domin ci gaba da rayuwa.

Har yanzu akwai mayakan Boko Haram da suka ki mika wuya ga hukumomin Najeriya.
Har yanzu akwai mayakan Boko Haram da suka ki mika wuya ga hukumomin Najeriya. AFP
Talla

Sai dai tuni al’ummar da rikicin Boko Haram ya shafa da shugabannin jama’a suka bayyana ra'ayoyi mabanbanta, inda wasu ke ganin cewa, ya kamata gwamnati ta yi taka-tsan-tsan a wannan shirin domin kuwa ba zai haifar da 'da mai ido ba a cewarsu.

Sai dai wasu na da ra'ayin cewa, tun da tsoffin mayakan na Boko Haram sun tuba, to ya kamata al'umma su rungume su a  matsayin 'yan uwansu mutananen kirki domin a cewarsu, rashin karbar su a cikin al'umma ka iya haddasa wata masifar.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Bilyaminu Yusujf daga birnin Maiduguri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.