Isa ga babban shafi

Ƴan ta'adda sun yaudari gwamnatin Buhari - Garba Shehu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi bayani akan yadda ‘Yan ta’adda suka yaudari gwamnatin sa wajen ganin ta biya musu bukatun su domin sakin fasinjojin jirgin kasan da akayi garkuwa da su, amma daga bisani suka ki sakin su.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, 2022
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, 2022 © Bashir Ahmad
Talla

Jaridar Premium Times ta jiwo mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu na bayyana cewar, gwamnati ta biya bukatun da ‘Yan ta’addan suka gabatar mata, ciki harda sakin matan su da ‘yayan su da aka tsare, amma kuma sai su suka ki cika na su alkawarin na sakin fasinjojin.

Jirgin kasar Najeriya da 'yan ta'adda suka kaiwa hari
Jirgin kasar Najeriya da 'yan ta'adda suka kaiwa hari © Daily Trust

Sakin mata da jarirai

Shehu ya bayyana cewar daga cikin wadanda aka sake harda matar daya daga cikin shugabannin ‘Yan ta’addan da jira jiran ta guda biyu da ta haifa a asibiti, bayan sakin wasu yara guda 7 da suka bukata.

Jaridar ta jiyo kakakin shugaban kasar na cewar, bayan sakin wadanda ake tsare da su din, gwamnati tayi safarar su ta jirgin sama daga Adamawa zuwa inda aka mika su ga ‘yan ta’addan, amma kuma sai suka shafawa idan su toka, suka ki sakin fasinjojin.

Kudin fansa

Mai magana da yawun shugaban kasar yace gwamnati ba zata bada kudi ga Yan ta’addan ba, kuma zata ci gaba da iya bakin kokarin ta wajen kubutar da sauran mutane 31 da ake rike da su.

Shugabannin sojin Najeriya
Shugabannin sojin Najeriya © Bashir Ahmad

Fasinjoji 9 suka mutu lokacin da aka kaiwa jirgin hari, yayin da sauran wadanda akayi garkuwa da su suka biya makudan kudade kafin a sake su.

Janyewar mai shiga tsakani

Rahotanni sun ce mai shiga tsakani domin sasantawa tsakanin Yan ta’addan da gwamnati Tukur Mamu ya janye saboda abinda ya kira barazanar hallaki shi da akeyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.