Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda na kafa gwamnati a Kaduna - El Rufa'i

Gwamnan Jihar Kaduna dake Najeriya, Malam Nasir Ahmed El Rufai ya rubutawa shugaban kasar Muhammadu Buhari wasika, inda yayi korafin cewar 'yan ta’adda na iko da wasu yankunan jihar sa, abinda ke tabbatar da matsalar tsaron da ake fama da ita a Jihar.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i. © Twitter@GovKaduna
Talla

A wasikar da Gwamna Nasir El Rufai ya rubutawa shugaban kasar domin janyo hankalin sa akan halin da ake ciki a jihar Kaduna, Gwamnan yace 'yan ta’addar na ci gaba da iko akan wasu yankunan jihar wajen kafa gwamnati irin na su da kuma sansanin kai hare hare a yankin.

Jaridar Premium Times da ake wallafawa a kasar tace, El Rufai ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin wata wasika da ya rubuta masa a karshen watan Yuli, inda yake cewa 'yan ta’adda na samun ci gaba wajen mayar da dazukan jihar a matsayin sansanin da suke amfani da shi wajen kai hare hare a jihohin dake yankin Arewa ta Yamma, kamar yadda bayanan tsaro na asiri suka tabbatar.

Gwamnan yace daga cikin ayyukan da wadannan 'yan ta’adda ke yi harda saka dokar hana harkokin siyasa da kuma yakin neman zaben shekara mai zuwa a kauyukan Madobiya da Kazage.

Wasikar ta kuma bayyana yadda 'yan kungiyar Ansaru suka dinga gudanar da bukukuwan aure a yankin Kuyello dake karamar hukumar Birnin Gwari, bikin da ya samu halartar mutane da dama.

Jihar Kaduna na daya daga cikin yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya, da 'yan bindiga suka zafafa hare hare, yayin da a watan jiya suka yi barazanar sace Gwamna El Rufai da shugaban kasar Muhammadu Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.