Isa ga babban shafi

Najeriya: Masu ruwa da tsaki sun amince da sake gina babbar kasuwar Jos

Gwamnatin Jihar Filato dake Najeriya ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki tsakanin al’ummar Jihar da zummar fadakar da su akan matakan da take dauka na sake gina babbar kasuwar Jos da kuma ribar da Jihar zata samu.

Gwamnan jihar Filato kenan, Simon Lalong
Gwamnan jihar Filato kenan, Simon Lalong © PLSG
Talla

Wannan matakin, ya biyo bayan adawar da wasu al’ummar jihar keyi da aikin wanda ake saran Bankin Jaiz ya gudanar da kudin sa, kana ya tafiyar da shi na wasu shekaru kafin mallakawa gwamnati.

Yayin jawabi ga taron fitattun 'yan Jihar da gwamnati ta kira, Gwamna Simon Lalong yace sake gina kasuwar na daga cikin manyan ayyukan da yayi alkawari lokacin yakin neman zaben sa, domin dawo da martabar birnin Jos da kuma dawo da baki da masu yawon bude ido kamar lokacin da aka saba a baya, kafin konewar kasuwar shekaru 20 da suka gabata.

Lalong yace gwamnati tare da bangarori da dama da kuma masu zuba jari domin gudanar da aikin, amma sharuddan da aka gindayawa sun saba da Muradin jihar, kafin Bankin Jaiz ya gabatar da na shi tayin, na sanya kudin sa kashi 100 wajen gina kasuwar da kuma yadda za’a raba shagunan dake ciki kashi 60 da 40 da kuma lokacin da za’a kwashe kafin mayar da kudin su da kuma mallakawa gwamnati kasuwar.

Gwamnan yayi watsi da sanya siyasa da addini cikin lamarin, inda wasu ke zargin cewar za’a mikawa bankin Musulunci kasuwar har tsawon shekaru 40.

Yayin da yake tsokaci a wajen taron, tsohon Gwamnan mulkin Soji, Admiral Samuel Bitrus Atukum, wanda a lokacin jagorancin sa shugaban kasa na soji na wancan lokaci Janar Muhammadu Buhari ya bude kasuwar ya bukaci ci gaba da tuntuba da kuma yiwa jama’a bayani domin fahimtar matakan da gwamnati ke dauka da kuma halin da ake ciki.

Dan majalisar tarayya yayi watsi da irin cece kucen da suka biyo bayan shirin sake gina kasuwar wanda ya danganta shi da siyasa, inda yace babu dalilin yin haka ganin cewar bayan gina kasuwar duk wani dan jihar dake bukatar shago na da hurumin gabatar da bukatar sa domin ganin an bashi.

Sanarwar Daraktan yada laraban gwamnatin jihar Dakta Makut  Simon Macham ya rabawa manema labarai tace, Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya Rabaran Polycarp Lubo da wakilin kungiyar Jama’atu Nasril Islam Sani Mudi sun bayyana goyan bayan su na ci gaba da aikin gina kasuwar.

Yunkurin sake gina kasuwar dai ya gamu da adawa mai zafi daga wasu jama’ar jihar saboda rawar da Bankin Jaiz zai taka, abinda ya kaiga wasu barazanar zuwa kotu domin hana aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.