Isa ga babban shafi

Najeriya: Buhari ya ba da wa'adin makonni 2 a kawo karshen yajin aikin ASUU

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya baiwa ministan ilimi Adamu Adamu wa’adin makonni biyu da ya kawo karshen dogon yajin aikin da malaman jami’oi ke yi, wanda yanzu haka ya shiga watanni 5.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AP - Bayo Omoboriowo
Talla

Rahotanni sun ce shugaba Buhari ya bada wannan umurni ne bayan karbar rahotan kwamitoci da ma’aikatu da kuma bangarorin da ke kokarin kawo karshen yajin aikin.

Shugaban kasar ya gayyaci jami’an wadannan hukumomi ne domin karbar cikakkun bayanai a kan halin da ake ciki dangane da yajin aikin.

Kungiyar malaman jami’oi ta ASUU ta tsunduma cikin yajin aiki a ranar 14 ga watan Fabrairu domin neman ganin gwamnatin kasar ta biya musu bukatun su, abin da ya katse harkokin bada ilimi gaba daya a jami’oin gwamnatin tarayya da kuma na jihohi, yayin da daga bisani sauran kungiyoyin kwadago dake jami’oin suma suka bi sahu.

Yanzu haka hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasar NLC ta bukaci daukacin rassan ta da su shirya tsunduma yajin aiki a makon gobe domin goyan bayan malaman, kuma tuni bankuna da ma’aikatan tashoshin jiragen sama da ma’aikatan gwamnati suka bayyana shirin shiga yajin aikin gadan gadan kamar yadda aka bukace su.

Daga cikin wadanda suka shiga ganawar da shugaban kasar yayi da wakilan hukumomin gwamnati akan yajin aikin harda ministan ilimi Adamu Adamu da ministar kudi Dr Zainab Ahmad da takwaranta na kwadago Chris Ngige da na sadarwa Isa Ali Ibrahim Pantami da Sakataren gwamnati Boss Mustapha.

Masu sanya ido a kan harkokin ilimi tare da iyayen yara na zargin gwamnatin Buhari da gazawa wajen shawo kan matsalolin bangaren ilimin da kuma biyan malaman hakkokin su domin ganin an janye yajin aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.