Isa ga babban shafi

Manoman Birnin Gwari sun biya ‘yan bindiga harajin miliyoyin naira

Bayanai daga yankin Birnin Gwari dake jihar Kaduna a Najeriya sun ce akalla naira miliyan 400 manoma suka biya 'yan bindiga cikin shekaru biyu, domin ba su damar yin aiki a cikin gonakinsu, amma duk da haka ba su tsira ba.

Alamar 'Yan bindiga masu kashe mutane babu kakkautawa a Najeriya
Alamar 'Yan bindiga masu kashe mutane babu kakkautawa a Najeriya © Daily Trust
Talla

Daya daga cikin shugabannin al’ummar yankin Alhaji Zubairu Abdura’uf ya shaidawa sashin Hausa na RFI cewa, idan har mahukunta ba su bar al'umma sun kare kansu ba, toh lalle kuwa za'a iya fuskantar matsalar karancin abinci a wannan shekara.

AbduRra’uf ya kara da cewa a shekarun baya manoman yankin Birnin Gwari na samar da abincin da yawansa ya kai akalla tan 700 na hatsi, amma a yanzu tuni labara ya sha banban la’akari da cewar mutanen bas a iya zuwa gonakinsu.

Birnin Gwari na daga cikin yankunan da suka fi fuskantar hare-haren 'yan bindiga a jihar Kaduna mai fama da matsalar tsaro a sassanta, inda 'yan ta'addan suka addabi mazauna yankin ta hanyar kashe rayuka da satar mutane domin karbar kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.