Isa ga babban shafi

Jamus za ta maidawa Najeriya kayan tarihin tsohuwar masarautar Benin

Jamus ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fara mayar da daruruwan kayayyakin tarihi na tagulla mallakin tsohuwar masarautar Benin, zuwa Najeriya, matakin da ya zama kokari mafi girma daga wata kasa ta Turai wajen mayar da muhimman kayayyakin tarihin da ta kwace a lokacin mulkin mallaka.

Daya daga cikin kayan tarihin tsohuwar masarautar Benin dake gidan adana kayan tarihi na Hamburg dake kasar Jamus.
Daya daga cikin kayan tarihin tsohuwar masarautar Benin dake gidan adana kayan tarihi na Hamburg dake kasar Jamus. AP - Daniel Bockwoldt
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Jamus Annalena Baerbock da ministar al'adu Claudia Roth ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar da takwarorinsu na Najeriya a birnin Berlin, bayan da Jamus ta bayyana cewa za ta fara maido da kayayyakin tarihin na tagulla tun a shekarar bara.

Tuni mahukuntan na Jamus suka mika ababen tarihi guda biyu a jiya Juma’a ga takwarorinsu na Najeriya, da suka hada da, kan wani sarki da wani allo da ke nuna mayaka uku.

Dubban kayayyakin tarihi na tagulla mallakin tsohuwar masarautar Benin da a yanzu ke Najeriya ne, ke ajiye bazu a cikin gidajen tarihi na sassan Turai, bayan da Turawan mulkin mallaka suka yi awon gaba da su a karshen karni na 19.

Kididdiga ta nuna cewar, Jamus kadai tana da adadin kayayyakin tarihin da suka kusan 1,100, wadanda aka kera a karni na 16 zuwa na 18, wadanda aka raba tsakanin wasu gidajen tarihi 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.