Isa ga babban shafi

Alkalin Alkalan Najeriya Mai shari'a Ibrahim Tanko ya yi murabus

Rahotanni daga Najeriya sun ce alkalin alkalan kasar Mai shari’a Ibrahim Tanko ya mikawa shugaba Muhammadu Buhari wasikar murabus dinsa daga bakin aiki yau litinin.

Alkalin alkalan Najeriya Mai shari'a Ibrahim Tanko Muhammad.
Alkalin alkalan Najeriya Mai shari'a Ibrahim Tanko Muhammad. NAN
Talla

Cikin wasikar da Mai shari’a Ibrahim Tanko ya mikawa shugaba Buhari ya bayyana matsalar lafiya a matsayin babban dalilin da ya tilasta masa murabus.

Sai dai murabus din na mai shari’a Tanko na zuwa a dai dai lokacin da zarge-zargen rashawa ya dabaibaye shi bayan wata wasika da alkalan kotun koli 14 suka sanyawa hannu da ke nuna yadda alkalin alkalan ke tafka rashawa.

 Tuni dai shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da sunan Mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin mukaddashin alkalin alkalan Najeriyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.