Isa ga babban shafi

Nigeria: Buhari ya nada sabbin ministoci guda 7

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada sabbin ministoci guda 7 domin maye gurbin wadanda suka aje mukaman su a watan jiya domin tsayawa takarar zaben shekara mai zuwa.

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari © Bashir Ahmad
Talla

Wasikar da shugaban ya aikewa Majalisar Dattawa domin amincewa da sabbin ministocin ta kunshi sunayen Umana Okon Umana daga Jihar Akwa Ibom da Henry Ikechukwu Ika daga Jihar Abia da Adewole Adegoruye daga Jihar Ondo.

Sauran sun hada da Odum Udi daga Jihar Rivers da Goodluck Nnana Opia daga Jihar Imo da Umar Ibrahim El-Yakub daga Jihar Kano da kuma Joseph Ukama daga Jihar Ebonyi.

 Tsayawa takara

Daga cikin ministocin da suka aje mukaman su domin tsayawa takarar zabe akwai Rotimi Amaechi da Godswill Akpabio da Ogbonnaya Onu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.