Isa ga babban shafi

Najeriya: Kotun Koli ta amince da amfani da Hijabi a Makarantun Legas

Kotun kolin Najeriya ta baiwa dalibai mata musulmi a jihar Legas damar sanya hijabi a makarantu ba tare da wata tsangwama ko nuna musu wariya ba.

Wau daliban maranta sanye da hijabi a birnin Kano dake Najeriya.
Wau daliban maranta sanye da hijabi a birnin Kano dake Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Hukuncin na kutun kolin Najeriya dake Abuja wannan Jumma’a na amatsayin wani gagarumin ci gaba ga hakkokin mutunta addinai a Lagos dama kasar baki daya.

Alkalai shida cikin bakwai suka amince

Daga cikin alkalan da suka halarci zaman kutun na daga ita sai Allah ya isa, akwai mai shara’a Olukayode Ariwoola da Kudirat Kekere-Ekun da John Inyang Okoro da  Uwani Aji da Mohammed Garba, da Tijjani Abubakar, sai kuma Emmanuel Agim.

Cikin alkalan bakwai, shida suka amince da amfani da hijabi a makarantun na Lagos yayin da daya ya ki amincewa da matakin.

Haramcin sanya hijabi

Tun cikin watan Fabrairun 2017 ne gwamnatin jihar Legas ta ruga kotun koli domin kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a ranar 21 ga watan Yulin, 2016, wanda ya amince wa dalibai musulmai su yi amfani da hijabi a makarantun firamare da sakandare na gwamnati a Legas, bayan rusa hukuncin haramcin sanya hijabin da wata kotun lagos din ta yi a watan Yunin shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.