Isa ga babban shafi

EFCC ta kama Yari tsohon gwamnan Zamfara kan badakalar biliyan 80

Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta kama tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari dangane da binciken da ake yiwa Akanta Janar na kasa Ahmed Idris saboda zargin karkata kudin da ya kai naira biliyan 80.

Jigo a jam'iyyar APC kuma tsaohon gwamnan Zamfara Abdul Aziz Yari
Jigo a jam'iyyar APC kuma tsaohon gwamnan Zamfara Abdul Aziz Yari © ©abdul aziz yari
Talla

Wani jami’in Hukumar ya tabbatarwa Jaridar Daily Trust kama tsohon gwamnan tare da Anthony Yaro, shugaban wani kamfani mai zaman kan sa dangande da badakalar da ake tuhumar Idris.

Kakakin hukumar Wilson Uwajiram ya tabbatar da kama tsohon gwamnan.

Tun 16 ga watan Mayu EFCC ta kama Akanta Janar na Najeriya Ahmed Idris bisa zarginsa da almundahana ta naira biliyan 80.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.