Harin jirgin kasa: 'Yan ta'adda sun sake wata fasinja mai juna biyu
A Najeriya ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan na da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, sun sallami wata mace mai juna 2 daga cikin fasinjojin.
Wallafawa ranar:
A wani hoton bidiyo da wata jaridar kasar ta samu, matar, wadda ba a bayyana sunata ba, ta yi kira ga gwamnatin kasar ta tattauna da ‘yan ta’addan don ceto rayuwar wadanda suka saura a hannunsu.
Ta ce masu garkuwar sun ba su kulawa da ta dace, ta wajen ciyarwa da kula da lafiyarsau.
Jaridar ‘Daily Nigerian’ da ake wallafawa a kasar ta ruwaito wata majiya na cewa ba a biya kudi fansa a kan matar mai juna biyu ba.
Majiyar ta kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa wata mata ta haihu a sansanin ‘yan ta’addan.
gwamnatin tarayyar Najeriya ta sha alwashin kubuto fasinjoji 60 da ke hannun ‘yan ta’addan, wadanda suka shiga hannunsu a ranar 28 ga watan Maris, amma har yanzu babu wani zance mai karfi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu