Isa ga babban shafi
Najeriya-Sufuri

Jiragen sama za su daina aiki a Najeriya daga Litinin saboda tsadar mai

Kamfanonin sufurin jiraagen sama a najeriya sun sanar da dakatar da ayyukansu daga ranar Litinin mai zuwa sakamakon tashin gwauron zabbi da man jirgin sama ya yi zuwa Naira 700 a kan kowace lita, su na mai jajantaw fasinjoji.

Jirgin kamfanin ARIK.
Jirgin kamfanin ARIK. Laurent Errera/Wikimedia Commons
Talla

Sun bayyana haka ne a cikin wata wasika da shugaban kungiyar masu kamfanonin sufurin jiragen sama,  Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina, ya aike wa da ministan sufurin jiragen sama  Hadi Sirika.

A cikin wasikar Sarina ya ce man jirgin sama ya tashin daga Naira 190 duk lita zuwa naira 700 a yaanzu, inda ya ce babu wani kamfanin sufurin jirgen sama da zai iya jure wannan karin frashi.

‘Yan Najeriya sun shiga zaman zullumi sakamakon kudirin karin farashin albarkatun man fetur da hukumomin kasar suka dauka, lamarin da ya janyo tada jijiyoyin wuya tsakaninta da kungiyoyin kwadago.

A halin yanzu dai ana sayar da litar man diesel, wanda akasarin manyan motocin daukar kaya ke amfani da shi a kan sama da naira dari 6, lamarin da ya haddasa tsadar farashin kayayyakin masarufi a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.