Isa ga babban shafi

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya fara ziyara a Najeriya

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya sauka a Najeriya domin ziyarar kwanaki 2.

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayin gaisawa da Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum tare da tawagarsa, ranar 3 ga Mayu, 2022.
Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayin gaisawa da Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum tare da tawagarsa, ranar 3 ga Mayu, 2022. © REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Bayan saukarsa, Guterres ya ziyarci jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar, yankin. da har yanzu kef ama da matsalar hare-haren mayakan Boko Haram da na ISWAP da suka balle daga kungiyar.

Yayin ziyarar tasa a Borno, sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya gana da gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum a birnin Maiduguri, daga bisani kuma ya gana da wasu daga cikin iyalan da rikicin Boko Haram ya shafa tsawon fiye da shekaru 10.

Daga jihar ta Borno, Antonio Guterres ya tashi zuwa birnin Abuja,  inda zai gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

A birnin na Abuja ana sa ran Guterres ya jagoranci wani bikin alhini da kuma karrama wadanda suka rasa. rayukansu yayin harin bam din da aka kai kan ginin Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2011. Daga nan kuma zai gana da wakilan kungiyoyin mata da matasa, da kuma shugabannin addinai da ‘yan jarida.

Wannan dai shi ne karo na farko da Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ke ziyartar Najeriya tun bayan hawansa kan mukamin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.