Mutane 11 sun jikkata a harin bam din da aka sake kaiwa Taraba
Rundunar ‘yan sanda a Taraba, ta ce harin bam din da aka kai kan wata mashaya a jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya ya yi sanadin jikkatar mutane 11, da suka hada da maza 10 da kuma mace 1.
Wallafawa ranar:
Bam din ya tashi ne a mashayar da ke unguwar Nukkai a wajen Jalingo, babban birnin jihar da misalin karfe 7 na daren ranar Juma'a da ta gabata, kamar yadda kakakin 'yan sanda Usman Abdullahi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Kakakin ‘yan sandan y ace bayanan da suka tattara sun nuna cewar, wani mutum da ba a gano wanene ba ne ya ajiye bam din cikin jakar leda a mashayar kafin daga bisani ya tarwatse.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai, wani bam ya fashe a wata mashaya da ke garin Iware, inda mutane 6 suka mutu wasu 16 kuma suka jikkata.
Kwana guda bayan faruwar lamarin ne kuma kungiyar ISWAP ta dauki alhakin kai harin, abinda ke zama alamar farko ta bayyanar ta a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya, sabanin wuraren da ta saba kai hare-hare a yankin tafkin Chadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu