Isa ga babban shafi

Sojin Najeriya da Nijar sun kashe gwamman mayakan ISWAP a Tafkin Chadi

Jiragen yakin Najeriya da Nijar sun yi wa ‘yan ta’adda ruwan bama-bamai a yankin Tafkin Chadi, inda suka samu nasarar kashe matyakan kungiyar ISWAP akalla 70.

Wani jirgin yakin Najeriya.
Wani jirgin yakin Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Kakakin rundunar sojin saman Najeriya Edward Gabkwet ya ce, sun kaddamar da farmakin hadin gwiwa da Nijar kan mayakan na ISWAP daga ranar 13 ga Afrilun nan, bayan gano ‘yan ta’addan da dama a yankin na Tafkin Chadi da ya hada iyakar najeriya da Nijar.

Yankin tafkin Chadi ya shahara wajen zama matattarar mayakan ISWAP, kungiyar masu ikirarin jihadi tun shekarar 2016.

A tsawon lokacin da suka shafe suna kai hare-hare tare da abokan hamayyarsu Boko Haram, bangarorin biyu sun kashe mutane fiye da dubu 40 a cikin shekaru goma da suka gabata, kuma sama da mutane miliyan biyu ne ke gudun hijira saboda tashe-tashen hankula da ake ci gaba da yi.

Tun a shekarar da ta gabata, mayakan ISWAP da suka balled aga kungiyar Boko Haram suka kara samun karfi,  bayan mutuwar tsohon jagoransu uwar kungiyar Abubakar Shekau, wanda ya rasa ransa a sakamakon rikcin cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.