Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

Iyalai sun lashi takobin hana sufurin jirgin kasa har sai an ceto 'yan uwansu

‘Yan uwan ​​mutanen da ‘yan ta’adda suka sace a harin da suka kaiwa jirgin kasa akan hanyar Abuja zuwa Kaduna a Najeriya, sun gargadi hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta kasar NRC, da kada ta koma aikin jigilar fasinjoji har sai an sako ‘yan uwansu da aka yi garkuwa da su.

Jirgin kasan da 'yan ta'adda suka kaiwa hari akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Jirgin kasan da 'yan ta'adda suka kaiwa hari akan hanyar Abuja zuwa Kaduna. © AP
Talla

Yayin da yake Magana a wurin taron da suka a Juma’ar nan da ta gabata a Kaduna, shugaban kungiyar ‘yan uwan ​​mutanen da aka sace, Dakta Abdulfatai Jimoh, ya ce rashin mutuntaka ne jirgin kasa ya cigaba da aiki tsakanin Abuja zuwa Kaduna, yayin da wadanda aka sace ke ci gaba da zama a cikin daji.

Iyalan fasinjojin da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su, sun kuma sha alwashin kawo cikas ga ayyukan jirgin kasa a tsakanin Abuja da Kaduna muddin ba a amsa bukatarsu ba.

A ranar 28 ga watan Maris ‘yan ta’adda suka kaiwa jirgin kasa hari bayan dasa bam akan titinsa, a yayin da yake  kan hanyar zuwa Kaduna daga Abuja, inda mutane da dama suka mutu, baya ga wasu fiye da 100 da ba a gano su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.