Isa ga babban shafi
Najeriya - 'Yan bindiga

Sama da mutum dubu 400 sun tsarewa hare-haren Filato na baya-bayan nan

Hukumomi a Najeriya, sun ce, sama da mutum dubu hudu da dari takwas ne suka tserewa gidajensu, sakamakon hare-haren da masu dauke da makamai suka kaddamar a Filato da ke tsakiyar kasar.

Alamar 'Yan bindiga masu kashe mutane babu kakkautawa a Najeriya
Alamar 'Yan bindiga masu kashe mutane babu kakkautawa a Najeriya © Daily Trust
Talla

Ana zargin ‘yan bindiga da ke kara kaimi a jihohin tsakiya da arewa maso yammacin kasar da hannu wajen kai hare-haren.

Shugabannin al’ummar yankin guda biyu da kwamandan rundunar ‘yan banga na yankin sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an kashe mutane sama da 100 a ranar Lahadin da ta wuce a wasu kauyuka da dama.

Kayan agajin gaggawa

Ministar kula da jin kai ta kasar, Sadiya Umar Farouq ta ce ta bayar da umarnin a kai kayan agaji cikin gaggawa da suka hada da abinci da ruwa da barguna da gidajen kwana na tanti ga wadanda rikicin ya rutsa da su.

Kakakinta Nneka Ikem Anibeze wadda ta fitar da sanarwar ta ce an kai hari a kauyuka biyar da suka hada da Kyaram, Gyambau, Dungur, Kukawa, Shuwaka da ke karkashin gundumar Garga, abin da ya tilastawa mutum sama da 4,800 tserewa, wadanda akasarinsu mata ne da kananan yara.

Baza ayi wa 'yan bindiga sassauci ba - Buhari

Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa ba za a yi wa wadanda suke da hannu a hare-haren da ake kaiwa sassan kasar sassauci ba, yayin da ake kara matsin lamba ga hukumomin da abun ya shafa domin dakile matsalar tsaro.

A ranar Larabar da ta wuce ma an jiyo gwamnan jihar Benue, na cewa, an kashe mutane 24 a wasu hare-hare biyu da ‘yan bindiga suka kai a jiharsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.